Philippines

Guguwar Goni da ta hallaka mutane 7 a kasar Philippines ta nufi Taiwan

Mutanen da guguwar Hagupit ta rutsa dasu cikin kasar Philippine a shekarar bara
Mutanen da guguwar Hagupit ta rutsa dasu cikin kasar Philippine a shekarar bara REUTERS/Erik De Castro

A kalla mutane 7 ne suka mutu, yayin wasu dubunnai suka tsere zuwa tudun mun tsira, sakamakon mahaukaciyar guguwar Goni, da tsananin ruwan sama suka auka wa arewacin kasar Philippines.

Talla

Wannan kuma ya haifar da ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa, inda kuma wasu mutanen 2 suka bace, yayin 4 suka samu raunuka.
Guguwar Goni na gudun KM 165 a kowace sa’a, inda ta nufi arewa maso gabashin lardin Cagayan, kuma yau Asabar jami’an gwamnatin kasar suka ce an tserar da a kalla mutane 1,200.

A kasar Taiwan, inda guguwar ta Goni ta nufa kuwa, an kwashe maki 'yan yawon bude ido a kalla 1,700.

Suma mahukuntan China sun bayyana cewa akwai alamar Guguwar ta Goni zata isa kasar, sai dai kuma zai yi wuya tayi wani mummunan ta'adi, kamar yadda hukumar kula da yanayin kasar ta bayar da sanarwa.

A Japan kuwa, an bayyana yuwuwar dakatarwa, dama soke sauka da tashin jiragen sama, a lokacin da ake hasashen isar guguwar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.