Isa ga babban shafi
Lebanon

Firiya Ministan Lebanon ya yi bazaranar Murabus

Firiya Ministan Lebanon Tammam Salam
Firiya Ministan Lebanon Tammam Salam Reuters/Jamal Saidi
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Firiya Ministan Lebanon Tammam Salam ya yi barazanar yin murabus daga mukamin sa saboda yadda Masu zanga zangar adawa da gwamnatin ke ci gaba da karawa da Yan Sanda kasar.

Talla

Su dai masu zanga-zangar na nuna bacin ran su kan yadda gwamnati ta kasa kwashe tarin sharar da suka cika musu tituna.

A cewar hukumar agajin ta Red cross sama da mutane 16 ne suka jikata, yayin da aka raunata jami’an tsaro 35.

Kamfanin dilanci labaran Faransa AFP ya rawaito cewa sama da matasa 200 ne suka yi kokarin fin karfin Jami’an tsaro inda su ke amfani da kwalabe da duwastsu wajen jifansu.

Yanzu dai haka Lebanon ba ta da shugaban kasa da kuma Majalisa saboda matsalar siyasar da kasar ke fama da shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.