Isa ga babban shafi
Gabas ta tsakiya

Yake-yake sun hana wa yara da dama karatu a gabas ta tsakiya

wasu yara kanana
wasu yara kanana Reuters/路透社
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed | Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da kananan yara miliyan 13 rikicin gabas ta tsakiya ya hana zuwa makaranta, a wani al’amari da ta ke gargadi illar da haka zai yi haifarwa a nan gaba, muddin ba a fara nazarin hanyar shawo kan matsalar ba cikin gaggawa.

Talla

A wani rahotan da ta fitar kan illolin da rikicin ke haifarwa a gabas ta tsakiya, assuna kula da ilimin kanana yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya bayyana yadda rikece-rikece a yankuna 6 na gabas ta tsakiya, suka yi mumunan tasiri kan ilimi, inda su ka ce a yanzu haka akwai makarantu kusan 9,000, da rashin zaman lafiya ya hanasu zaman makaranta domin daukan darrusa.

Darakata majalisar a gabas ta tsakiya Peter Salama, yace yaki yafi yiwa kanana yara illa, wadanda dama ke rasa rayukansu a kan hanyarsu ta zuwa makaranta, wasu lokutan ma suna makarata ake kai musu harin dake iya hallaka su.

A shekarar da ta gabata sau 214 ana kai hare-hare a makarantu Syria, Iraq, Libya da yankin Falasdinu, Sudan da Kuma Yemen. Sai dai kuma abin yafi tsananata a Syria da suka shafe kusan shekaru 4 da rabi ana yaki.

Rahotan ya kuma bayyana cewa sama da malaman makarantu 52,000 rashin zaman lafiya ya tursasawa tserewa, lamarin da shima ya taka rawa wajen durkushewar ilimin kananan yara.

Majalisar Dinkin Duniya dai na cigaba da bayyana fargabanta kan makomar daliban da nan gaba ba a san halin da za su tsinci kansu ba, muddin rashin zaman lafiya ya gagara samuwa a yankin.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.