Isa ga babban shafi
Iraqi

Kungiyar IS ta kashe mutane 14 a Iraqi

IS na da'awar kafa daular Islama a yankin gabas ta tsakiya
IS na da'awar kafa daular Islama a yankin gabas ta tsakiya REUTERS/Thaier al-Sudani
Minti 1

Kungiyar IS mai da’awar jihadi a yankin gabas ta tsakiya ta kashe mutane akalla 14 tare da jikkata 55 a wani hari da ta kaddamar a yau a babban birnin Baghdad na Kasar Iraqi.

Talla

Kungiyar ta kai hain ne dandalin Wathba dake kusa da dandalin Tayran a tsakiyar birnin Baghdad.

Jim kadan da aukuwar lamarin,Kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai farmakin a wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumunta na Twitter, inda ta ce Mayakanta ‘Yan kunar bakin wake biyu ne suka kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.