Isa ga babban shafi
Falasdinawa-Israela

Rikici ya barke tsakanin Falestinawa da jami'an tsaron Israela a birnin Kudus.

matasan falestinawa ne ke tsintar duwatsu a matsayin makamin da suke tunkarar dakarun Israela dake da ingantatun makamai
matasan falestinawa ne ke tsintar duwatsu a matsayin makamin da suke tunkarar dakarun Israela dake da ingantatun makamai REUTERS/Ammar Awad
Zubin rubutu: Salissou Hamissou
Minti 2

Wani sabon rikici ya barke a yau lahadi tsakanin Falestinawa da jami’an tsaron kasar Israela a harabar babban masallacin Baitul Mukadis, dake birnin Jerusalem ko Kudus, kamar yadda yan sandan israelar suka sanar, ana gobe a koma aiki bayan tafiya hutun sallar a Aid al Adha ko layya ga Musulmi

Talla

A cikin wata sanarwa rundunar ‘Yansandan a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa, wasu matasan Falestinawa ne suka fara jifar ‘Yansandan dake amfani da karfi wajen tarwatsa mutane a harabar masallacin, na Kudus masallacin dake da daraja ta uku ga musulmi, wanda suma Yahudawan ke dauka da daraja.

Shi dai faruwar irin wannan rikici tsakanin ‘Yansandan Israela da matasan Falestinawa a harabar ta babban Masallacin na Baitul Mukadis (Kudu) ba bako ba ne, inda ake samun taho mugama sakamakon turjiya daga matasan Falestinawa a gaban sojan mamayen kasar Izaela a wannan guri mai daraja, da ya kasance ruhin duk wani rikicin da aka share tsawon shekaru ana yi tsakaninsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.