Afghanistan

Sojin Afghanistan sun karbe Kunduz daga Kungiyar Taliban

Sojojin da suka kwace garin Kunduz daga hannun mayakan Taliban.
Sojojin da suka kwace garin Kunduz daga hannun mayakan Taliban. REUTERS/Stringer

Rundunar Sojin Afghanistan tayi nasarar kwace garin Kunduz daga hannun kungiyar Taliban bayan an kwase kwanaki uku ana dauki ba dadi a tsakanin su.

Talla

Rahotanni sun ce sojojin sun samu nasarar ne da taimakon sojin Amurka da suka dinga kai hare haren sama kan sansanin kungiyar Taliban, abinda ya baiwa sojojin damar shiga tsakiyar birnin a yau alhamis.

Mataimakin ministan cikin gida na Afghanistan Ayoub Salangi ya ce yanzu haka sojojin gwamnati ke da iko da birnin.

Tuni dai dakarun suka cire tutar da mayakan Taliban suka kafa a wani dandali dake birnin na Kunduz, inda kuma suka kafa tutargwamanati.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.