Afghanistan

Kungiyoyin agaji sun fice daga Kunduz

Cibiyar MSF a Kunduz na Afghanistan
Cibiyar MSF a Kunduz na Afghanistan REUTERS/Stringer

Majalisar dinkin duniya ta ce a halin da ake ciki yanzu dukannin kungiyoyin bayar da agaji sun fice daga birnin Kunduz na Afghanistan sakamakon harin Amurka kan asibiti kungiyar Likitoci ta MSF da kuma tarzoma d ake sake barkewa a kasar.

Talla

Mai magana a madadin Hukumar Bayar da agaji ta Majalisar dinkin duniya a Afghanistan Jens Laerke ta ce bangaran hukumar agajin Majalisar 2, da 4 na kungiyoyi dake zaman kansu, da kungiyar agajin kasa da kasa 10 sun sauya sheka saboda rikicin kunduz da kuma rashin tsaro .

A ranar Assabar da ta gata ne Hare-hare Amurka a Kunduz kan Taliban ya ritsa kan asibitin kungiyar likitoci ta MSF tare da kashe mutane 22, batun dake ci gaba da jan hankulan duniya, inda kungiyar ta bayyana al ‘amarin a matsayin laifuka yaki da Amurka ta aikata.

Sai dai babban kwamanda sojin Amurka Janar John Campbell, a Afghanistan yayin amsa tambayoyi a gaban Kwamitin kula da aikin soji na majalisar dattawan kasar. ya ce harin ya auku ne a bisa kuskure.

Tuni shima dai sakatere janar na Majalisar dinkin duniya Ban ki-Moon ya bukaci gudanar da bincike kan hari.

Sama da mutane dubu 300 ke samun gajiyar taimakon asibiti kungiyar likotoci ta MSF a birnin kunduz kawai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.