Falasdin-Isra'ila

Ina goyon bayan gwagwarmayar Falasdinawa -Abbas

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Carlo Allegri

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya bayyana cewar yana goyan bayan gwagwarmaya cikin kwanciyar hankali, kan yaki da mamayar da Israila ta yiwa Yankunan su, bayan wani tahsin hankalin makwanni biyu da ya kai ga kashe mutane sama da 30.

Talla

A jawabin da ya yi ta kafar talabijin, shugaba Abbas ya bayyana cewar Falasdinawa suna da damar kare kan su daga duk wani hari da ake kai musu.

A bangare daya kuma Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya bukaci kwamitin sulhu ya duba matakin da Isra’ila ta dauka na killace Yankunan su.

Mansour ya bayyana matakin a matsayin wanda kan iya tada hankali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.