Syria

Gwamnatin Syriya ta kaddamar da gaggarumin hari a yankin Alepo

Wani Titi da ya ratsa tsakkiyar  birnin Alepo na kasar Syria da yakin basasa ya dai-daita
Wani Titi da ya ratsa tsakkiyar birnin Alepo na kasar Syria da yakin basasa ya dai-daita 路透社

A jiya juma’a gwamnatin kasar Syriya ta kaddamar da wani gagarumin hari dake samun tallafi daga jiragen saman yakin kasar rasha, a wani wuri dake kusa da birnin Alepo, domin sake karbe wata babbar hanya da ta hada manya biranen kasar.

Talla

A dai gefen kuma, kasar Turkiya mai makwabtaka da Syriya ta bayyana kakkabo wani irgin liken asirin kasar Rasha a cewar kasar Amruka, ikrarin da Rashar ta karyata

Rasha da ta kasance babbar kawa ta gani kashe ni ga gwamnatin Shugaba Bashar Al’assad  ta ce, jiragen yakinta sun kaddamar da hare-hare guda 650 a kan yankuna 450 na kasar ta Syriya, tun lokacin da ta fara kai hare-harenta kan mayakan Jihadin kungiyar Isis, da yan tawaye a kasar Syriya yau da kimanin makwanni 4 da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.