China-Taiwan

Shugabannin China da Taiwan sun gana da juna

Shugaban Xi Jinping yana tabewa da Shugaban kasar Taiwan Ma Ying-jeou a Singapore.
Shugaban Xi Jinping yana tabewa da Shugaban kasar Taiwan Ma Ying-jeou a Singapore. REUTERS

Shugabannin kasashen China da Taiwan sun gana da juna a karon farko tun yakin basasa da ya raba kasashen biyu, shekaru sama da 66. Shugaban China XI Jinping da takwaransa na Taiwan Ma Ying-jeou sun gama hannu na tsawon sama da minti guda, ala’amarin da ba a zaci zai faru ba a haduwar shugabannin biyu.

Talla

Shugabannin sun yi murmushi a lokacin da suke gaisawa da juna a gaban ‘Yan jaridu.

Wannan ne karon farko da Shugabannin bangarorin biyu suka hadu tun ballewar Taiwan daga China a 1949.

Sai dai zuwa yanzu babu wata yarjejeniya da aka bayyana shugabannin biyu sun cim ma a tsakaninsu bayan bude taron na China da Taiwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI