Turai-Turkiya

kasashen Turai za su yi taro da Turkiya kan Yan gudun hijira

wasu yan gudun hijirar Syriya a birnin Berlin na kasar Jamus
wasu yan gudun hijirar Syriya a birnin Berlin na kasar Jamus REUTERS/Stefanie Loos

Shugabannin kasashen Turai sun amince domin gudanar da taro da kasar Turkiyya kafin karshen wannan shekara da muke ciki ta 2015 da niyyar kawo karshen dimbin ‘yan cirani dake kwarara zuwa Turai.  

Talla

Shugaban Faransa Francois Hollande ya shaidawa manema labarai a wajen taro da suke yi a Malta cewa, zasu yi wannan taro ne tsakanin karshen wannan wata ko farkon watan gobe da kasar Turkiyya.

Acewar shima Shugaban Majalisar kungiyar Tarayyar Turai Donald Tusk zasu yi wannan taro, yayinda shima dai Shugaban Hukumar kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ke cewa, ya umarci mambobin kungiyar dasu ga lallai sun bada tasu gudunmawar kudi Euro biliyan 2.5 da zasu tara domin tallafawa Turkiyya cikin shekaru biyu, domin ta samu ta shawo kan bakin haure da ‘yan ci rani, miliyan 2 dake Turkiyya, yawanci daga Syria.

A cewar Hukumar kasashen Turai zata bada gudunmawar kudi Euro miliyan 500, domin a kai ga abinda ake nema Euro biliyan 3. A kokarin taimakawa shugaban Turkiyya ya shawo kan ambaliyar bakin haure.

Akalla bakin haure dubu 650 daga cikin dubu 800 da suka isa Turai ta teku, a bana ta kasar Turkiyya suka bi, kasar da ke da ‘yan gudun hijira akalla miliyan 2 daga Syria.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.