Syria-Lebanon

An yi musayar Fursunoni a Syria

REUTERS/Ammar Abdullah

Gwamnatin Lebanon ta yi musayar fursunoni tsakaninta da mayakan Al Nusra masu alaka da Al Qaeda a yau Talata inda mayakan suka saki wasu Sojojin kasar 16 da ‘Yan sanda.

Talla

Mayakan na Al-Nusra masu alaka da al Qaeda sun saki wasu Sojojin Lebanon 16 hada ‘Yan sanda da suke garkuwa da su tsawon shekara guda.

Gwamantin Beirut kuma ta saki wasu mambobin mayakan 13 da suka hada Saja al-Dulaimi tsohuwar matar shugaban mayakan IS Abu bakr al Bagdadi.

An nuna fursunonin a telebijin da dogon gemu suna shiga motocin kungiyar agaji ta red cross a lokacin da mayakan an nusra suka sake su.

An kuma nuna ‘yan uwan fursunonin na murna a Beirut wadanda suka jima suna zanga-zangar ganin an sake su.

Wannan dai na zuwa ne bayan mayakan nusra sun janye daga yankin Arsal da suka kwace tare da garkuwa da mutane 30.

Akwai wasu jami’an Sojin Lebanon 9 da ‘yan sanda da mayakan IS ke ci gaba da garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.