Syria

'Yan tawayen Syria sun fice daga birnin Homs

Hotan shugaban Syria Bashar al-Assad a birnin Homs
Hotan shugaban Syria Bashar al-Assad a birnin Homs REUTERS/Omar Sanadiki

‘Yan tawayen Syria sun fara ficewa daga yanki na karshe da suke rike da shi a birnin Homs karkashin wata yarjejeniyar tsagaita musayar wuta da suka cimma da gwamnatin kasar kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria ta sanar.

Talla

Yarjejeniyar wadda aka cimma a farkon wannan watan na Disamba, ta bukaci ficewar kimanin ‘yan tawaye 2,000 tare da iyalansu daga yankin Waer na birnin Homs.

Tuni dai motoci uku kirar bus suka fara kwashe mutane 150 daga yankin kamar yadda shugaban kungiyar wadda ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria, Rami Abdel Rahman ya sanar, kuma ya ce sama da mutane 700 na jiran a fitar da su a halin yanzu.

A baya dai an bayyana Homs a matsayin “birnin tawaye” kuma ya na daya daga cikin wuraren da suka fara bijire wa shugaban Syria Bashar al-Assad a shekara ta 2011.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.