Isa ga babban shafi
Saudiya

Mata sun shiga zaben Saudiya a karon farko

Fawzia al-Harbi, daya daga cikin 'Yan takara a zaben Saudiya
Fawzia al-Harbi, daya daga cikin 'Yan takara a zaben Saudiya REUTERS
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

An fara jefa kuri’a a zaben farko a tarihin kasar Saudiya da ya kunshi Mata ‘Yan takara da masu jefa kuri’a a yau Assabar.

Talla

Wannan ne karo na farko da Mata zasu kada kuri’a, sannan sama da 900 suka tsaya takara a zaben kananan hukumomi.

Maza kimanin 6,000 ke takara a zaben da kunshi yawan kujerun shugabanni 284.

Sai dai ana ganin yana da wahala matan su lashe zaben saboda dokokin Saudiya na haramta cudanya tsakanin maza da mata a waje guda.

Har yanzu dai a Saudiya an haramtawa Mata tukin Mota, sannan ba su iya fita balaguro sai da izini tare da rakiyar muharraminsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.