Isa ga babban shafi
China-Taiwan

Mace ta farko ta lashe zaben shugaban kasar Taiwan

Tsai Ing-Weng mace ta farko da ta samu nasarar lashe kujerar shugaban kasar Taiwan
Tsai Ing-Weng mace ta farko da ta samu nasarar lashe kujerar shugaban kasar Taiwan
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Shugabar ‘yan adawar Taiwan mai kyamar manufofin China, Tsai Ing-Wen ta lashe zaben shugabancin kasar da gagaarumin rinjaye yayin da ta kasance mace ta farko a tarihin kasar da ta samu irin wannan nasarar.

Talla

Dubban jama’a ne suka yi gangami tare da yin wasan wuta a shalkwatan jama’iayyar DPP ta Ing- Wen domin nuna farin cikinsu dangane da wannan nasarar wadda ta kawo karshen shugabancin jam’iyyar KMT mai kawance da China.

A jawabinta na farko da ta yi wa manema labarai, Ing-Wen ta gargadi cewa duk wani matsi daga gwamnatin China zai yi sanadiyar tabarbarewar dangantaka a tsakanin kasashen biyu, amma ta yi alkawarin tabbatar da zaman da China.

Kasar China dai ba ta farin ciki da nasarar da jam’iyyar DPP ta samu kasancewar ba ta goyon bayan manufofinta kamar yadda jam’iayyar KMT ke yi wadda ta mulki kasar cikin nuna amintaka da China.

Tuni dai China ta gargadi makwabciyarta Taiwan cewa, ta gaggauta yin watsi da duk wani kudiri na yunkurin neman 'yan cin dogaro da kai kamar yadda jam’iyyar DPP ke ikirari.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.