Saudiya-Lebanon

Saudi ta bukaci ‘Yan kasarta su fice Lebanon

Ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir
Ministan harkokin wajen Saudiya Adel al-Jubeir REUTERS/Faisal Al Nasser

Kasar Saudiyya ta umarci dukkan ‘yan kasarta da ke zaune a Lebanon da su fice su koma gida sakamakon sabani da ya sarke tsakanin kasashen biyu.

Talla

Saudiya ta dakatar da wani shirin ne da ta kulla don bai wa Lebanon kayan soja na kudi da ya kai dalar Amurka biliyan 3, don mai da martani game da wuraren da ‘yan kungiyar Hezbollah ke zaune.

Ita ma kasar Daular Larabawa aminiyar Saudiya ta dauki irin wannan mataki, na kiran ‘yan kasarta dake zaune a Lebanon su bar kasar.

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Waje na Saudiyya ta bayar tace saboda matsalolin tsaro ya sa ta hana ‘yan kasar tafiya Lebanon, sai idan tafiyan ya zama dole.

Sanarwan na cewa Saudiya na sake duba dangantakarta da Lebanon, saboda barazanar da take samu daga ‘yan kungiyar Hezbollah.

Saudiyya ta yi kukan cewa kungiyar Hezbollah na yin munanan farfaganda da halayen ta’addanci kan kasashen larabawa da kuma addinin musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.