Larabawa

Kasashen Larabawa sun saka Hezbollah cikin kungiyoyin ‘Yan ta’adda

Ministocin harakokin wajen kasashen Gulf a Saudiya
Ministocin harakokin wajen kasashen Gulf a Saudiya REUTERS/Faisal Al Nasser

Manyan kasashen Larabawa guda shida sun ayyana kungiyar Hezbollah ta Lebanon a matsayin kungiyar ‘Yan ta’adda a wani mataki da ake ganin na kaddamar da yaki da kungiyar, musamman sabaninsu akan rikicin Syria da Iran.

Talla

Kasashen Saudiya da Kuwait da Oman da Bahrain da Qatar da Daular larabawa ne suka amince da daukar matakin jefa Hezbollah a matsayin kungiyar ‘Yan ta’adda.

Kasashen dai na ganin Hezbollah a matsayin barazana, musamman shigar da yara ‘yan kasashensu ayyukan ta’addanci.

A watan jiya ne Saudiya ta dakatar da tallafin soji da ta ke ba Lebanon karkashin shirin Faransa na kudi da suka kai dala biliyan 3.

Yanzu haka kuma Saudiya na nazari akan huldarta da Lebanon daya daga cikin manyan aminnan Iran da suke takun saka.

Lebanon ta fito ta soki Saudiya a watan Janairu kan rikinta da Iran bayan kisan wani malamin Shi’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.