Turkey

Friministan Turkiya ya yi Murabus

Friministan Turkiya Ahmet Davutoglu
Friministan Turkiya Ahmet Davutoglu REUTERS/Umit Bektas

A wani al’amari na ba zata Friministan Turkiya Ahmet Davutoglu ya sanar da bukatar ajiye mukaminsa bayan sabanin da aka samu tsakaninsa da shugaba kasar Recep Tayeb Erdogan.

Talla

A ranar 22 ga watan Mayu da Jam’iyyar AKP zata gudanar da taron ta, Friministan Ahmet Davutoglu zai ajiye mukaminsa a hukumance.

Kamar dai yadda dokokin Jam’iyar ta tanada mutum guda ke iya rike mukamin shugaban jam’iyar dana Frimiya.

Kafin sanarwa ta yau alhamis, an ta samu rade-radin sabani dake akwai tsakanin Davutoglu da Shugaba Erdogan duk da cewa shugabanin biyu sun musanta hakan, sai a jiya ne komai ya bayyana.

Kokarin da aka yi na sasantasu a fadar gwamnatin kasar ya ci tura, da dama daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyar dai sun nuna takaicinsu kan wannan Baraka a jam’iyyar mai mulki ta AKP, yayin da wasu ke kwalla.

A wata ‘yar gajeriyar jawabi da ya yi gaban manema labarai, Davutoglu ya ce daukar wannan mataki ba a son ransa ba ne, amma zai ci gaba da bada gudumawa ci gaba jam’iyyar da gwamnatin Erdogan.

Sabanin tsakanin shugabanin biyu ya biyo bayan kin amincewa da Davutoglu ya yi da wasu tsare tsaren shugaba Erdogan a tafiyar da mulkin kasar.

Batun dake zuwa a dai-dai lokacin da Turkiya ke fama da tarin matsaloli da suka kunshi rikici da kungiyar ‘yan aware ta PKK da kuma kungiyar ISIL gami da matsalar bakin haure sama da miliyan 1 dake gibje yanzu haka a kasar.

A watan Augustan shekara ta 2014 ne aka rantsar da Ahmet Davutoglu a matsayin firai ministan kasar ta Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI