Korea ta arewa

An yi kiran a sassauta wa Koriya ta Arewa takunkumi

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na kallon yadda jami'ansa ke harba makami mai linzami
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un na kallon yadda jami'ansa ke harba makami mai linzami Reuters

Wasu mutane uku da suka karbi lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya a duniya sun bukaci a sassautawa Koriya ta Arewa takunkuman da kasashen duniya suka kakaba ma ta bayan sun ziyarci kasar.

Talla

Mutanen uku daga kasashen Norway da Birtaniya da Isra’ila sun ce sun gani da idonsu takunkuman sun yi tasiri matuka ga gurguncewar fannin lafiya a kasar bayan sun ziyarci wasu asibitotci da kuma cibiyoyin bincike.

Manyan kasashen duniya dai sun tsawwalawa Koriya ta Arewa takunkumi bayan ta bijerewa bukatunsu kan gwaje gwajen makaman nukiliya da dama ta dinga yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.