Indiya

Wata 'Yar Kasar Indiya ta yi Azumi na dole na tsawon shekaru 16

Malama Irom Sharmila
Malama Irom Sharmila rfi

Wata ‘yar kasar India mai rajin kare hakkin bil’adama ta kawo karshen yajin kin cin abinci da ta fara shekaru 16 da suka gabata.

Talla

Masu lura da lamurran duniya dai na ganin wannan shine azumi mafi tsawo da wani bil’adama ya taba yi, a duniya.

Malama Irom Sharmila da aka fi sani da jaruma na Manipur na adawa ne da zalunci da fin karfi da jami'an tsaro ke nunawa a arewa maso gabashin kasar tasu.

Ta yi ta sharban kuka a lokacin da aka banbare wani takunkumi data makalawa bakin ta domin a tilasta mata cin abinci ta hanci da baki.
'Yar shekaru 44, tsare ta aka yi saboda zargin ta nemi kashe kanta, katon laifi a kasar India, sannan aka kebe ta a wani asibiti da take jinya.

Jiya ne dai aka sake ta bayan da ta dauki alkawari a kotu cewa za ta kawo karshen azumin da take yi, inda nan take aka bada belin ta akan kudiun kasar India Rupee dubu goma, kwatankwacin Dollan Amurka 150.

Likitoci dai sunce tana bukatar a dubata sosai kafin ta fara sharban abinci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI