Syria-Amurka-Rasha

An kai hari kan Asibiti na karshe a Daraya

Asibitoci suna fuskantar barazana a Syria
Asibitoci suna fuskantar barazana a Syria REUTERS/Abdalrhman Ismail

Wata kungiyar masu kare hakkin dan’adam ta kasar Birtaniya da ke sa ido a Syria, ta ce Sojojin gwamnati da sun jefa bam kan asibitin fararen hula na karshe da ya rage a yankin Daraya da ke birnin Damascus. 

Talla

Kungiyar ta ce akwai kwakkwaran zaton cewa sojin gwamnati sun yi amfani da bam din Napalm, makamin da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta amfani da shi.

A baya kasar Amurka ta taba amfani da irin wannan makami da ke haifar ga konuwa ga wanda ya samu, a yakin da ta yi da kasar Viatenam.

Asibitin dai shi ne daya tilo da ke zama tallafi ga fararen hula 8,000 a yankin na Daraya da ke hannun ‘yan tawayen kasar.

Tun a baya masu rajin kare hakkin dan’adam sun yi ta sukar Sojojin Syria da na Rasha bisa zargin suna amfani da makaman da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta amfani da su wajen kai hari kan 'yan tawayen Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.