Isa ga babban shafi
Israel-Turkiyya

Isara'ila da Turkiya sun yi musayar Zafafan kalamai kan Gaza

AFP PHOTO / THOMAS COEX
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 Minti

Isra'ila da Turkiya sun yi musayar kalamai masu zafi bayan munann hare haren da Israilan ta kai Gaza sakamakon rokar da aka harba mata daga Yankin Falasdinawa.

Talla

Ranar Lahadi Isra’ilan ta kai hare-haren sama da 20 wanda ya kahse mutane 4 ya kuma raunanan wasu da dama.

Wannan ya sa Turkiya ta fitar da suka mai tsauri kan yadda aka kai harin kan fararen hula.

Turkiya tace mayar da huldar diflomasiya da Israila ba zai sa ta rufe idon ta lokacin da take kaiwa Falasdinawa hari ba.

Yayin da ita ma Isra’ila tace mayar da huldar ba zai sa ta yi shiru idan Turkiya ta soke ta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.