Jordan

An harbe wani marubuci da yayi batanci ga addinin Musulunci a Jordan

Motar asibiti da ke dauke da gawar Nahed Hattar
Motar asibiti da ke dauke da gawar Nahed Hattar REUTERS/Muhammad Hamed

Wani dan bindiga yau lahadi ya harbe sanannen marubuci dan kasar Jordan Nahed Hattar har lahira, a harabar wata kotu da yake fuskantar shari’ar yada wani zane na batanci ga addinin Musulunci. 

Talla

Dan bindigar dai ya dirkawa Hattar alburusai uku kafin jami’an tsaron Jordan su kama shi a harabar kotun dake yankin Abdali.

A ranar 13 ga watan Agustan da ya gabata, jami’an tsaron suka kama marubucin mai shekaru 56, bayan yada hoton batanci da yayi ga addinin musulunci, sai dai an bada belinsa a farkon watan Satumba, kafin halaka shi da dan bindiga yayi.

Har yanzu dai hukumar tsaron Jordan bata gano ainahin wanda ya kirkiri hoton batancin da Marubuci Hattar ya yada ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.