Isa ga babban shafi
Indonesia

An tsinci gawar Jariri a ban-dakin Jirgi a Indonesia

Jami'an kula tsabtar Jirgi
Jami'an kula tsabtar Jirgi Reuters
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Jami’an tashar Jirgi a Indonesia sun sanar da tsintar gawar jariri a cikin ban-dakin Jirgin Qatar Airways bayan ya iso Jakarta daga Doha a ranar Lahadi.

Talla

Masu shara ne suka tsinci jaririn da aka nadidiye cikin takardar ban-daki. Kuma an bayyana cewa Jaririn bakwaini ne.

An kama wata Mata da ake zargin ita ta haifi jaririn, kuma yanzu haka ana gudanar da bincike akanta a asibiti.

Matar dai za ta fuskanci hukunci idan har binciken asibiti ya tabbatar da ita ce ta jefar da jaririn a ban-daki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.