Isa ga babban shafi
US-Yemen

Pentagon na cikin shirin ko-ta-kwana kan Yemen

Ana ci gaba da ruwan bama-bamai a Yemen
Ana ci gaba da ruwan bama-bamai a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon na cikin shirin ko-ta-kwana don kaddamar da sabbin hare-haren ramako kan mayakan Houthi da ke kasar Yemen. Wannan na zuwa ne bayan harin da mayakan suka kai kan jirgin ruwan yakin Amurka a ranar Lahadi da Laraba.

Talla

A jiya Alhamis kasar Amurkan ta kai harin makami mai linzami don lalata na’urorin da mayakan Houthi ke amfani da su wajen gano in da jirgin ya ke, a wani mataki na mayar da martani kan harin da mayakan suka ka iwa jirgin ruwan sojin Amurka a wannan makon.

Shugaba kasar Barack Obama, ya bayar da umarnin kaddamar da farmakin kan ‘yan tawayen na Houthi, kuma a karon farko kena da gwamnatin kasar ta bayar da irin wannan umarnin tun lokacin da aka fara yaikn Yeman.

A ranar Lahadi da laraba ne Mayakan sun kai hare-haren makamai masu linzami kan jirgin sojin ruwan Amurka, yayin da mai magana da yawun Pentagon, Peter Cook ya ce, suma sun dauki matakin mayar da martani ne don kare ma’aikatansu da jiragen ruwansu da kuma yancinsu na yawo kan teku.

Hukumomin Amurka sun gargadi cewa, akwai yiwuwar nan gaba, mayakan Houthi su sake amfani da wata dabara wajen kai sabon hari kan jiragen ruwan Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.