Brazil

Fursunonni sun kashe kan su a rikicin gidan yari

Ana yawaita samun rikici a fursunonni Brazil
Ana yawaita samun rikici a fursunonni Brazil AFP PHOTO/SSP/ALLAN DE CARVALHO/HO

‘Yan sanda Brazil sun ce mutane 8 ne suka mutu a gidan yarin kasar bayan barkerwar rikici tsakanin fursunonni. Rikicin na zuwa ne kwana guda bayan rikici tsakanin kungiyoyi da basa ga maciji a wani gidan yari na daban a kasar ya lakume rayukan mutane 25. 

Talla

A gidan yarin Rondonia da ke arewa maso yammacin kasar jami’an ‘yan sanda sun ce an aiwatar da yanka rago tare da kona gawarwaki fursunonni.

Rahotanni sun ce rikicin ya barke ne lokaci da wani mai shari’a ya kai ziyarar domin sanin bukatun wadanda ake tsare dasu.

Wannan ba shine karo na farko da ake samun irin wannan tashin hankali a gidaje yarin kasar na Brazil ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI