Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan zata hukunta kafofin yada labaran da suka bijire mata

Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Kasar Pakistan ta haramta sanya duk wani abu da ke da alaka da India a kafafen yada labaran kasar, tare da gargadin duk kafa da ta sabawa umarnin zata fuskanci tsattsauran hukunci.

Talla

A watan satumban da ya gabata, dangantaka ta kara yin tsami tsakanin kasashen biyu, bayan harin da wasu ‘yan tawaye suka kai kan barikin sojin India a yankin Kashmir, inda suka kashe sojinta 18, harin da Indian ke zargin Pakistan ce ta goyi bayan kai sa.

Bayan harin ne dai India ta haramtawa wasu taurarin fina-finai ‘yan Pakistan aiki da masana’antarta ta shirya fina-finai wato Bollywood.

A jiya Juma’a ma sai da Rundunar sojin Indian ta ce ta kashe sojin Pakistan 7, a kan iyakar kasashen biyu da ke Kashmir, ikirarin da Pakistan ta karyata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.