Iraq

Dakarun Iraqi na fuskantar turjiya a Mosul

Ana cigaba da gwabza fada a Mosul
Ana cigaba da gwabza fada a Mosul

Dakarun Iraqi dake yunkurin kakkabe mayakan ISIS a Mosul na ci gaba da fuskantar turjiya daga mayakan, wadanda ke mayar da martini.

Talla

Rahotanni sun ce, sojoji tare da mayakan Kurdawa na cigaba da kutsa kai sassan birnin, Mosul, tare da taimakon hare haren saman jiragen yakin Amurka, yayin da mayakan na ISIS ke tada bama bamai, da kuma amfani da motoci dan kai harin kunar bakin wake.

Kakakin sojin Amurka Kanar John Dorrian, yace ya zuwa yanzu sunkai hare haren sama sau 32 tsakanin 17 ga watan da muke ciki zuwa 23, kan mayakan na ISIS.

A ranar Lahadin da ta gabata, mayakan suka yi yunkurin dauke hankali daga kan rashin nasarar da suke samu na Mosul, ta hanyar kai hari a wani kauye da ke kan iyakar Iraqi da Jordan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.