Isa ga babban shafi
UNICEF-Syria

UNICEF ta ce an kashe 'yan makaranta a Syria

Yankin Idlib, inda aka kai hare-hare kan dalibai a Syria
Yankin Idlib, inda aka kai hare-hare kan dalibai a Syria Reuters/路透社
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Hukumar UNICEF ta ce yaran makaranta 22 ne aka kashe tare da malaman su 6 lokacin da hare haren sama da ake kai wa Syria ya fada kan wata makarantar  da ke Yankin Idlib.

Talla

Daraktan UNICEF Anthony Lake ya bayyana wanann kazamin harin da aka kai kan makarantar yara a matsayin abin takaici, inda yake cewa babu abinda ya raba shi da laifufukan yaki.

Lake ya ce da gangan aka kai harin, ganin cewar ba sau daya aka kai shi ba.

Kungiyar da ke sa ido kan rikicin Syria ta ce jiragen yakin da suka kai hari kan wannan makaranta kuma suka kashe daliban sun fito ne daga kasar Rasha ko kuma Syria.

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin ya yi Allah wadai da harin.

Samantha Power, Jakadiyar Amurka ta soki Rasha wadda ta ce taki hada kai da Majlisar Dinkin Duniya dan warware rikicin Syria, yayin da Kwamishinan Jinkai Stephane O’Brien ya bukaci daukan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.