India

Hazo ya hana mutane fita a Delhi

Ana Hazo a Delhi
Ana Hazo a Delhi REUTERS/Adnan Abidi

An rufe daukacin makarantu tare da dakatar da ayyukan gine-gine a Delhi sakamakon hazo da ya turmuke babban birnin kasar na India. An dauki matakin ne don kare lafiyar al’umma da kan iya shakar gurbataccen iska.

Talla

Akwai Abubuwa da dama da ake ganin su suka haifar da hazon da yanayi mai dauke da gurbataccen iska wanda ya turmuke birnin na Delhi.

Manoma suka yi kunar tattakar amfanin gona bayan girbi a jihohi da dama a India musamman wadanda ke makwabtaka da Delhi da kuma bikin Diwali da ya kara gurbata muhallin birnin inda miliyoyan mutane suka yi ta harba abun wasan wuta.

Sai dai kuma ana ganin yanayin na bana ya zarce yadda aka saba gani inda hukumomin lafiya suka yi gargadi cewa yanayin hazon barazana ne ga lafiyar al’umma da kan iya janyo cututtuka da suka shafi huhu da zuciya.

An bayyana ma’aunin hazon ya kai 500 inda kowa a garin na Delhi na iya kamuwa da cututtukan da suka shafi numfashi, wanda akan ya sa aka bukaci kowa ya kasance a gidansa.

An dai rufe makarantu a birnin na Delhi na tsawon kwanaki 3 tare da dakatar da yyukan gine gine na kwanaki 5.

Rahotanni sun ce dubban mutane ke jerin gwano domin sayen kyallen da za su toshe hancinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.