Iran

Iska mai gurbata muhalli ta hana zirga-zirga a Tehran

Iska mai gurbata muhalli ta hana zirga-zirga a Tehran
Iska mai gurbata muhalli ta hana zirga-zirga a Tehran Reuters/路透社

Hukumomin kasar Iran sun bukaci al’ummar birnin Tehran da su zauna a gidajensu har sai an kwantar da kurar da ta mamaye daukacin birnin hakazalika an rufe makarantun birnin na wani lokaci ganin irin barazanar da ke tattare da wannan iskar mai gurbata muhalli.

Talla

Magajin garin Tehran Mohammad Bagher Ghalibaf ya ce an dauki matakai na shawo kan al’amarin tare da bayar da umarnin rufe masa’antu da ake sarrafa siminti da kamfanonin da ke fasa dutse.

An yi hasashen iskar za ta soma washewa nan da jibi laraba inda ake sa ran al’ummar birnin sama da miliyan goma sha hudu za su soma fitowa don ci gaba da rayuwa ba tare da fuskantar wata barazana ba.

A shekarar 2014 kusan mutane dari hudu aka kwantar a asibiti sakamakon cututuka da suka shafi numfashi bayan sun shaki gurbatacciyar iska.

Tun daren jiya lahadi kurar mai iska ta soma mamaye Tehran babban birnin kasar ta Iran.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.