Isa ga babban shafi
Isra'ila

Majalisar Dinkin Duniya ta soki shirin Isra'ila kan yankin Falasdinawa

Sabbin gidajen da gwamnatin Isra'ila ta gina a Yamma da kogin Jordan
Sabbin gidajen da gwamnatin Isra'ila ta gina a Yamma da kogin Jordan
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Majalisar Dinkin Duniya tace yunkurin kasar Isra’ila na halarta gina gidaje 4,000 a yankunan Falasdinawa dake gabar yamma da kogin Jordan haramtacce ne, domin ya sabawa dokokin duniya.

Talla

Babban jami'i na ofishin kare hakkin Bil Adama na Majalisar, Zeid Ra’ad ya bukaci Majalisar Israila ta sake tunani akan matakin wanda yace zai bata sunanta a idanun duniya.

Yanzu haka Yahudawa 400,000 ke zama a gabar yamma da Kogin Jordan wanda yanki ne na Falasdinawa.

Majalisar Dinkin Duniya, Amurka da kuma Tarayyar Turai duk sun bayyana matakin a matsayin yunkurin soke shirin kafa kasar Falasdinu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.