Syria

Dubban mutane na komawa Aleppo

Hukumar kula da 'Yan gudun hijira na tallafawa Mutanen Aleppo  na Syria
Hukumar kula da 'Yan gudun hijira na tallafawa Mutanen Aleppo na Syria REUTERS

Dubban mutane na komawa gidajensu a birnin Aleppo na arewacin Syria, sakamakon zaman lafiyar da aka sama bayan da dakarun gwamnati suka kwace garin daga hannun ‘yan tawaye.

Talla

Garin Aleppo wanda ke kunshe da kusan mutane miliyan biyu kafin barkewar yaki a Syria yanzu ya kasance kamar an yi ruwa an dauke sakamakon kazamin artabun da aka yi tsakanin ‘yan tawaye da kuma dakarun gwamanati a tsawon shekaru kusan shida.

A cikin wannan mako kawai sama da iyalai dubu biyu ne suka koma garin na Aleppo kamar dai yadda shugaban ofishin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya a yankin na Aleppo Sajjad Malik ya tabbatar.

Jami’in ya ce mutane na ci gaba da komawa gidajensu, kuma an bude shaguna da dama a birnin, duk da cewa an lalata mafi yawa daga cikin gine-ginen da ke cikinsa.

Sai dai kamar yadda rahotanni ke cewa, jama’a na rayuwa ne a cikin mawuyacin hali, sakamakon sanyin huturu da kuma karancin makamashin wutar lantarki da kuma iskar gas, yayin da wasu ke rayuwar a cikin gidajen da ba su kofofi balantana taga.

Wata babbar matsalar da jama’ar birnin ke fuskanta a halin yanzu ita ce rashin ruwan sha mai tsafta.

A shekara ta 2012 ne dai ‘yan tawaye suka kama birnin na Aleppo, kuma sai a watan Disamban da ya gabata ne dakarun Bashar Assad tare da taimakon Rasha suka yi nasarar kwace birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI