Bakonmu a Yau

Dr Ahmad Dukawa: Binciken cin zarafin dan'adam a kasar Myanmar

Sauti 03:23
'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar suna dakon samun izinin isa ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kuala Lumpur a Malaysia
'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar suna dakon samun izinin isa ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kuala Lumpur a Malaysia

Majalisar dinkin duniya ta ce tawagarta ta masu bincike kan tauye hakkin dan’adam, zata bincika zargin cin zarafin Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar. Ana kuma sa ran fara aikin tawagar masu binciken a ranar Litinin mai zuwa. Kasashen Duniya dai na cigaba da sukar gwamnatin Myanmar karkashin Aung San Suu Kyi da nuna halin ku in kula da kisan da sojin kasar ke wa ‘yan kabilar ta Rohingya. Kan wannan, Nura Ado Suleiman, ya tattauna da Dr Sa’idu Ahmed Dukawa, tsohon shugaban sashin nazarin kimiyyar siyasa, a Jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya