Myanmar

Tawagar kare hakkin dan'adam zata fara aikinta a Myanmar

'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar suna dakon samun izinin isa ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kuala Lumpur a Malaysia
'Yan gudun hijira daga kabilar Rohingya Musulmi daga Myanmar suna dakon samun izinin isa ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke Kuala Lumpur a Malaysia

Majalisar dinkin duniya ta ce tawagarta ta masu bincike kan tauye hakkin dan’adam, zata fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafin Musulmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Talla

Ana sa ran fara aikin tawagar masu binciken a ranar Litinin mai zuwa.

Kasashen Duniya dai na cigaba da sukar gwamnatin Myanmar karkashin Aung San Suu Kyi, wadda ta taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel, da nuna halin ko in kula da kisan da sojin kasar ke wa ‘yan kabilar ta Rohingya.

Tun a watan Oktoban da ya gabata ne, sojin Myanmar suka mamaye jihar Rakhine da ‘yan Kabilar ta Rohingya suka fi yawa, inda suka rika cin zarafin al’ummar wajen hadi da yiwa mata fyade, kamar yadda rahotanni suka tabbatar, lamarin da ya tilastawa dubban ‘yan kabilar tserewa zuwa makwabtan kasashe.

Sai dai kuma har yanzu rundunar sojin kasar, tana cigaba da musanta zargin ta cin zarafin dan’adam tare da kare matsayinta da cewa tana kokari ne wajen murkushe wasu ‘yan ta’adda da suka kaiwa shingayen bincike na jami’an tsaro hari, a watan Oktoba da ya gabata a Jihar ta Rakhine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.