Syria

‘Yan tawayen Syria za su halarci tattaunawar sulhu

'Yan tawayen Syria za su tattauna da Gwamnatin Bashar al'Assad
'Yan tawayen Syria za su tattauna da Gwamnatin Bashar al'Assad AFP SANA / AFP

Kungiyoyin ‘yan tawayen Syria, sun amince su halarci tattaunawar sulhu tsakaninsu da gwamnati, tare da jaddada aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a fadin kasar. Za’a yi taron ne karkashin jagorancin Rasha da Turkiya, a babban birnin kasar Kazakhstan, Astana, a ranar 23 ga watan Janairu 2017.

Talla

Muhd Alloush jagoran bangaren 'yan tawayen Jaysh al-Islam ya bayyana matsayar da suka cim ma, ya-yin da ya ke sanar da cewa shi ne zai jagoranci tawagar da za ta wakilci 'yan tawayen a taron na Astana.

A wannan karon dai babu kasar Amurka cikin wadanda za su jagoranci tattaunawar sulhun. Ko da ya ke Ministan harkokin waje na Turkiya Mevlut Chavusglu ranar assabar din da ta gabata ya ce mai yiwuwa ne su gayyaci Amurka.

‘Yan tawayen na Syria sun amince da halartar taron ne bayan tattaunawar tsawon kwanaki 5 da suka yi da wakilan Rasha a birnin Ankara na Turkiya.

Taron na Astana zai maida hankali ne kan tabbatar yarjejeniyar Tsagaita wuta a ilahirin kasar Syria, ba da damar isar da kayayyakin agaji ga sassan kasar da aka gaza yin haka a baya, da kuma tattauna batun sakin mayakan ‘yan tawaye da sojin gwamnati suka kama.

Idan har taron na Birnin Astana ya yi nasara, zai bada Karin kwarin gwiwa ga taron da Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta a birnin Geneva don warware rikicin Syria.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI