Syria-Rasha-Turkiya

Za'a fara tattaunawar sulhu kan rikicin Syria a Astana

Mayakan 'yan tawayen Syria na kungiyar Jaysh al-Islam a kauyen al-Rayhan kusa da kauyen Douma dake kusa da birnin Damascus
Mayakan 'yan tawayen Syria na kungiyar Jaysh al-Islam a kauyen al-Rayhan kusa da kauyen Douma dake kusa da birnin Damascus Reuters/路透社

A ranar Litinin mai zuwa gwamnatin Syria zata fara tattaunawar sulhu da ‘yan tawayen kasar karo na farko a birnin Astana na Kazakhstan, bayan shafe shekaru shida da barkewar yaki a Syrian.

Talla

Za’a dai a gudanar da wannan tattaunawa karkashin jagorancin kasashen Rasha, Turkiya da kuma Iran.

A ranar Alhamis din da ta gabata shugaban Syria bashar Assad ya jaddada bukatar ‘yan tawayen na Syria su ajiye makamansu kafin amfana da shirin afuwa da gwamnati zata yi musu.

An dai gayyaci tawagar da zata wakilci sabon shugaban Amurka Donald Trump wajen tattaunawar sulhun a Birnin Astana, sai dai har yanzu bas u sanar da cewa ko zasu halarci taron ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.