Isa ga babban shafi
Syria

A gobe za a shiga wani sabon yinkurin samar da zaman lafiya a syria

mayakan yan tawayen à Alepo, a ranar  16 désemba 2016, na jiran a kwashesu daga birnin mai tarihi.
mayakan yan tawayen à Alepo, a ranar 16 désemba 2016, na jiran a kwashesu daga birnin mai tarihi. REUTERS/Abdalrhman Ismail
Zubin rubutu: Salissou Hamissou
Minti 2

A yauLitinin ne gwamnatin Syria da ‘yan tawayen kasar za su gana gaba-da-gaba a birnin Astana na Kazakhstan da nufin karfafa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da za ta kai ga magance rikicin tsawon shekaru shida.Wakilan kasashen Rasha da Turkiya da Iran da kuma Majalisar Dinkin Duniya na cikin mahalarta tattaunawar.  

Talla

A ranar 8 ga watan Fabairu mai zuwa ne ake saran Majalisar Dinin Duniya ta sake shirya wata tattaunawar shiga tsakani a birnin Geneva, bayan wadda za a gudanarwa a yau Litinin a birnin Astana da zimmar kawo karshen artabu tsakanin dakarun gwamnatin Syria da kuma ’yan tawayen kasar.

Tattaunawar ta gobe na matsayin wani gagarumin yunkurin kawo karshen yakin shekaru kusan shida da ya dai daita kasar, abin da kuma ya haddasa asarar rayuka kusan rabin miliyan, baya ga tilasta wa rabin al’ummar kasar kaurace wa muhhallansu.

Shugaban Syria Bashar al Assad ya ce, ya yi amanna wannan tattaunar za ta share fagen samar da yarjejeniyar sulhu da ‘yan tawayen kasar.

Suma ‘yan tawayen sun ce, za su mayar da hankali kan goyon bayan tsagaita musayar wuta a duk fadin kasar.

Kasar Rasha da ke goyon bayan gwamnatin Assad, it ace ta shirya zaman na yau, kuma hakan na zuwa ne bayan ta taimaka wa dakarun kasar da kuma mayakan da ke samun goyon bayn Iran samun nasarar karbe gabashin Aleppo a cikin watan jiya, abin da ake kallo a matsayin galaba mafi girma da aka samu kan ‘yan tawayen na Syria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.