Syria

Rasha da Turkiya da Iran sun amince da shirin tsagaita wuta a Syria

Taron sassanta Rikicin Syria a Astana na Kazakhstan
Taron sassanta Rikicin Syria a Astana na Kazakhstan REUTERS/Mukhtar Kholdorbekov

Kasashen Rasha da Turkiya da Iran sun amince da shirin tsagaita wutar rikicin Syria, yayin da suka sanar da shirin sanya ido dan ganin ana aiwatar da ita.

Talla

Bayan kwashe kwanaki biyu ana tafka mahawara, ministan harkokin wajen Kazakhstan Kairat Abdralmanov ya ce manyan kasahsen su amince su kafa wani kwamitin hadin gwiwa da zai tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar tsagata wutar da kuma hana barkewar wani tashin hankali.

Rahotanni sun ce an samu barkewar fada tsakanin bangarorin 'Yan tawayen da suka hada da Jabhat Fateh al Sham da Free Syrian Army.

Babban mai shiga tsakani daga bangaren gwamnatin Syria, Bashar al Jabari ya ce zasu ci gaba da ruwan wuta kan 'yan tawayen da ke Yammacin Damascus.

Taro na kwanaki biyu  don warware rikicin Syria a Astana ya samu halartan wakilai daga bangaren ‘yan tawaye da kuma bangaren Gwamnati, sai dai ba lallai ya kai ga kawo karshen yakin kasar ba.

'Yan tawaye sun ce Gwamnatin Syria da kasar Iran ya kamata a zarga da laifin sukurkucewar duk wani sulhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI