Syria

Mutane 40 sun mutu a harin bam a birnin Homs

Gidan talabijin na gwamnatin Syria ya nuna hoton harin da ya hallaka mutane 32 a birnin Homs.
Gidan talabijin na gwamnatin Syria ya nuna hoton harin da ya hallaka mutane 32 a birnin Homs. HO / AL-IKHBARIYAH AL-SOURIYAH / AFP

Jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai a ginin jami’an tsaron Syria dake a birnin Homs ya hallaka mutane 40 ciki har da babban jami’in leken asirin sojin kasar dake wannan yankin.

Talla

A rahotan da Kafar talabijin ta gwamnati ta fitar kuwa ta ce mutane kusan arba’in da biyu ne suka mutu baya ga tarin jama’ar da suka sami munmunar rauni a harin.

Tuni dai wata kungiya mai ikirarin jihadi da ake kira Tahrir Al-sham ta dauki alhakin kai harin na yau asabar a birnin na Homs da ke karkashin ikon gwamnati tun shekarar 2015.

Kungiyar ta kuma ce ita ta tura mayakanta biyar don kaddamar da harin kunar bakin waken.

Gwamnatin Syria ta yi alkawarin mayar da martani kan wannan harin dake zuwa a daidai lokacin da ake zaman taron sassanta rikicin kasar karkashin jagorancin wakilan gwamnati da na ‘yan adawa a birnin Geneva.

Akalla mutane sama da 400,000 aka kashe a yakin da ake ci gaba da fafatawa a kasar, yayin da kowanne bangare ke dagewa sai ya samu biyan bukata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI