Myanmar

Mutane 160 aka kashe a rikicin Myanmar

Fafatawa a jahar Shan ya yi sanadiyar rayuka fiye da 160.
Fafatawa a jahar Shan ya yi sanadiyar rayuka fiye da 160. DR

Rahotanni daga Myanmar sun ce akalla mutane 160 suka mutu a cikin watanni 3 sakamakon fafatawar da akayi tsakanin sojojin kasar da ‘yan wata kabila da ke dauke da makamai a Jihar Shan.

Talla

Rahotan ya ce mutane sama da 20,000 yanzu haka sun rasa matsugunin su sakamakon tashin hankalin da aka samu kusa da iyakar China.

Rundunar sojin Myanmar ta ce sojoji 74 aka kashe a fadan tare da ‘Yan Sanda 15 sai kuma ‘yan bindigan 13 da da wasu fararen hula 13.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI