China

Mutanen Jiangbei a China na kashe aurensu don samun kudin diyyar gida

Lardin Jiangsu a China
Lardin Jiangsu a China DR

Rahotanni daga China sun ce Ma’aurata fiye da 160 a lardin Jiangsu suka amince su kashe aurensu domin samun kaso mai tsoka na diyar gidajensu da gwamnati za ta rusa.

Talla

Ma’auratan sun gano cewa za su iya samun sabbin gidaje guda biyu da Karin kudi $19,000 idan har suka gabatar da kansu a matsayin wadanda ba su da aure.

Gwamnati China ta gina sabbin gidaje saboda kauyawan na Jiangbei da ke Lardin Jiangsu da nufin raya yankin.

Ma’auratan za su yarda su rabu da juna a hukumance don samun kaso mai tsoka maimakon gabatar da kansu a matsayin masu aure. Sai daga baya ne za su dawo su sake kulla aure a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI