Isra'ila

Wanzuwar sojin Iran a Syria barazana ce – Netanyahu

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu REUTERS/Abir Sultan/Pool

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce a ranar Alhamis mai zuwa zai gana da shugaban rasha Vladimir Putin a birnin Moscow, game da yunkurin da ya ce kasar Iran na yi na kafa sansanin soji na din din din a kasar Syria.

Talla

Tun bayan barkewar yakin Syria Isra’ila ke zargin kasar Iran da neman amfani da wannan dama wajen kafa sansanonin sojin ruwa ko na kasa, a kasar ta Syria.

To sai dai Iran ta sha musanta zargin, da kuma kare kanta da cewa, sojojinta sun shiga Syria ne don kare muhimman wuraren ibada na mabiya mazhabar Shi’a.

Kasar Isra’ila da basa ga miciji da Iran, na taimakawa gwamnatin Basharal-Assad da sojoji da kuma makamai, a kokarin da gwamnatinsa ke yi na murkushe tada kayar bayan ‘yan tawayen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.