Iraqi

Iraqi : Mutane 200,000 sun tsere Mosul

Hukumar Kula da Bakin Haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan wadanda suka gudu domin tsere wa yakin da ake gwabzawa a birnin Mosul na kasar Iraqi, a halin yanzu ya zarta mutane dubu 200.

Dubban mutanen Mosul na tserewa fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin Iraqi da mayakan IS
Dubban mutanen Mosul na tserewa fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin Iraqi da mayakan IS REUTERS
Talla

Sama da dubu 45 daga cikin wannan adadi sun baro birnin ne a cikin mako daya a cewar hukumar.

Hukumar ta ce a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata an samu karuwar wadanda ke tserewa fadan daka ake yi a birnin da ke arewacin Iraqi.

Rahoton ya ce daga ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata zuwa jiya lahadi, akalla mutane dubu 45 ne suka fice daga unguwannin da ke yammacin birnin sakamakon tsanantar fada a tsakanin mayakan IS da kuma sojojin gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya.

Hukumar IOM ta ce lamarin yana matukar tayar da hankula, lura da cewa a ranar 28 ga watan jiya kawai sama da mutane dubu 17 ne suka fice daga Mosul, yayin da wasu dubu 13 suka bar birnin a ranar asabar da ta gabata saboda tsanantar fada.

Da dama daga cikin mutanen da ke tserewa daga birnin na a cikin mawuyacin hali, sakamakon yadda kungiyoyin agajin suka gaza isa a gare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI