Koriya ta arewa ta yi gwajin makamai 4
Wallafawa ranar:
Amurka ta yi kakkausar suka dangane da gwajin makamai masu linzame da Koriya ta Arewa ta yi guda hudu a yau Litinin, gwajin da ya saba wa kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.
Gwamnatin Kim Jong-un ta sha alwashin samar da manyan makamai masu linzami da kan iya ka iwa Amurka, matakin da Trump ya ce ba zai taba faruwa ba.
Mai magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Mark Toner, ya bayyana a wata sanarwa cewa Amurka za ta ci gaba da daukar tsauraran matakai akan Koriya tare da kasancewa a cikin shirin domin kare Amurkan da kawayenta daga barazanar Pyongyang.
Koriya ta arewa dai ta mayar da martani ne ga atisayen da Sojojin Koriya ta kudu da Amurka suka a makon da ya gabata.
Koriya ta Arewa ta harba makaman ne arewacin Pyongan da ke gabas da teku cikin Japan da Koriya ta kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu