Afghanistan

Magoya bayanmu ne suka kai harin Afghanistan- IS

Kungiyar IS ta ce, magoya bayanta ne suka kai hari a wani asibitin soji da ke birnin Kabul na kasar Afghanistan a wannan laraba, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 30.

Jami'an tsaron Afghanistan sun kashe maharan asibitin sojin kasar
Jami'an tsaron Afghanistan sun kashe maharan asibitin sojin kasar REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun shiga wannan asibiti ne sanye da fararen kaya irin wadanda jami’an kiwon lafiya ke sanyawa, kuma an kawo karshen bata-kashi tsakanin maharan da kuma jami’an tsaro bayan da aka kashe illahirin ‘yan bindigar.

Kazalika wannan harin ya jikkata mutane fiye da 50 kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar.

Shugaban Afghanistan Asraf Ghani ya ce, harin wanda mutane hudu suka kai a asibitin mai gadaje 400, na a matsayin cin mutunci bil'adama.

Ghani ya kara da cewa, ana daukan asibitoci a matsayin tudun mun tsira kuma kadddamar musu da hari tamkar kaddamar da hari ne kan ilahirin kasar ta Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI