Isra'ila

Isra'ila na shirin kafa dokar takaita kiran Sallah

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a Ofishinsa da ke Jerusalem.
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a Ofishinsa da ke Jerusalem. REUTERS/Abir Sultan/Pool/File Photo

Majalisar kasar Israila ta amince da shirin farko na wata doka da zata taikaita kiran Sallah a Masallatai da kuma amfani da lasifika wajen kiran Salla a fadin kasar.

Talla

Dokar wadda zata fara aiki daga karfe 11 na dare zuwa karfe 7 na safe, zata tsallake wasu shinge uku nan gaba kafin ta zama doka.

Kafin dai amincewa da dokar saida aka tafka mahawara mai zafi, har wasu ‘yan Majalisu daga bangaren Larabawa suka yayyaga shafunan dake dauke da dokar.

‘Yan Majalisu 55 suka amince da dokar matakin farko yayin da 48 suka ki amincewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.