Iraqi

An gano kabari makare da gawarwaki a Iraqi

ISIL ta aikata mugan ayyuka a yankunan Mosul
ISIL ta aikata mugan ayyuka a yankunan Mosul REUTERS/Suhaib Salem

Jami’an sa kai a Iraqi da ke taimakawa Gwamnati sun sanar da gano wani wagegen kabari cike makare da daruruwan gawarwaki mutane da mayakan IS suka yiwa kisan gilla a kusa da birnin Mosul.

Talla

Kabarin da aka gano a gidan yarin Badush, rahotanni sunce IS ta kashe sama da mutane 600 lokacin da ta kwace ikon tafiyar da gidan yari a shekarar 2014, baya ga daruruwan mutane da tayi garkuwa dasu akasari mata.

Kungiyar Humar right Watch, ta ce IS ta yi amfani da daman da ta samu a wannan lokaci, tare da tursasawa fursunonin fararen hula shiga rami kafin bindige su.

Kungiyar ta ce ayyukan ta'addanci IS ba a gidan yarin kawai ya tsaya ba domin ta shiga gari inda ta diga kama mata tana garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.