Koriya na dakon martanin Park da aka tsige
‘Yan Koriya ta Kudu sun zura wa fadar Blue House idanu don ganin irin martanin da shugaba Park Geun-hye da aka tsige daga karagar mulki za ta mayar .
Wallafawa ranar:
A jiye ne dai kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta tabbatar da tsige Park saboda samun ta da hannu a wata badakala da ta shafi aminiyarta Cho Soon-sil.
Kotun dai ta yanke hukuncin ne a dai dai lokacin da shugabar ke kallon talabijin a wani dakinta na musamman da ke fadar Blue House.
A karon farko kenan da aka tsige wani shugaban Koriya da Kudu da aka zaba ta hanyar democradiya.
Wannan kuma na zuwa ne bayan an zargi Park da hannu wajen mara wa kawarta baya don tirsasa wa wasu kamfanoni bada miliyoyin kudade ga wasu cibiyoyi masu zaman kansu.
Kazalika an zargi shugabar da bai wa aminiyarta Soon-sil damar mu'amala da takardun sirri na gwamnati.
Sai dai masu taimaka wa shugaba Park Geun-hye sun ce, kawo yanzu, Park ba ta da shirin fitar da sanarwa da za ta nuna amincewa ko akasin haka da wannan hukunci na kotu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu