Saudiya-Japan

Sarki Salman na ziyara a Tokyo

Sarki Salman Bin Abdulazizi Al-Saud na ziyarar a Japan
Sarki Salman Bin Abdulazizi Al-Saud na ziyarar a Japan REUTERS/Toru Hanai

Sarki Salman na Saudiya zai gana da Firaministan Japan Shinzo Abe a yau Litinin a Tokyo a wata ziyarar farko da wani sarkin Saudiya ya kai Japan a tsawon shekaru 50.

Talla

Sarki Salman ya isa Japan da tawagar mutane sama da 1000 a ziyarar da ya ke yi a kasashen yankin Asia domin karfafa huldar kasuwanci tsakaninsu.

Sarki Salman ya isa Japan da tawagarsa sama da mutane 1000, kuma Tun a jiya Lahadi Japan ta tanadi masauki a manyan ote otel na birnin Toktyo domin tawagar Sarkin na Saudiya da zai yi kwanaki uku yana ziyara a kasar.

Yariman Japan mai jiran gado Naruhito shi ya tarbi Sarki Salman bayan saukarsa a filin jirgin Haneda a Tokyo, tare da yin tanadin manyan daruruwan motocin kasaita kirar Limosines domin tawagar Sarkin.

A yau ne kuma ake sa ran Sarki Salman zai gana da Firaministan Japan Shinzo Abe kan batun inganta huldar kasuwanci tsakaninsu.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da Sarkin Saudiya ya kai a Japan a tsawon shekaru 50 tun a 1971 zamanin Sarki Faisal.

Tuni dai Sarki Salman ya kai ziyara a Malaysia da Indonesia, kuma yanzu daga Japan zai nufi China kafin ya wuce zuwa Maldives, inda zai fuskanci bore yan adawa da ke kyamar ziyararsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.